Abubakar
Gumi ya warware alkawari
Daya daga cikin Malaman da aka yi wadannan zama
dasu Shaykh Sharif Ibrahim Saleh Maiduwuri, Allah ya ja kwanana, ya rubuta a
wani littafi nasa na Larabci mai suna"المغير" a mukaddima shafi na (29) ga fassarar a cikin
Hausa: “daga cikin sharuddan
da a ka gindaya a karshen wannan taro a Sokoto sune: kada wani daga cikin
malaman ya yi gaban kansa wajen buga ko yada abubuwan da a ka gabatar a wurin
zaman da a kayi. amma da Malam Abubakar Gumi ya dawo Kaduna sai ya warware alkawari
ya tarjama nasa jawabin zuwa Hausa, ya yada ta ta Gidan Rediyon (B.B.C) London (Musulunci da abin
da ya ke warware shi) daga cikin abin da ya ke warware musulunci akwai karanta
(Salatul Fatihi) saboda – a cewar sa - Shaihu Ahmadu Tijjani yana fifitata akan
karanta Alkur’ani”.
Wannan shine dalilin da ya sa shima
Shaykh Sharif Ibrahim Saleh ya buga nasa littafin da ya kaddamar a wurin
taron mai suna:
"التكفير أخطر بدعة تهدد السلام والوحدة بين المسلمين في نيجيريا".
Wanda aka buga shi kamar yadda a ka kaddamar da
shi a Larabcen shi, haka shi ma Shaykh Malam Nasiru Kabara ya yi, ganin Malam
Abubakar Gumi - Almajirinsa- ya warware alkawari a kan abin da aka cimma, sai shima ya sa aka
buga Littafin da ya kaddamar a wurin taron mai suna"حقيقة التصوف الإسلامي".
Haka Gwamnatin Soja ta Obasanjo da Shehu Musa
‘yar Aduwa ta shude ba ta iya magance sabanin da Malam Abubakar Gumi ya haifar
ba a wannan kasar na sai an koma kan
akidar dan Abdul Wahab a nan Najeriya sannan za a zauna lafiya.
Wannan ittifaki na malamai wanda aka yi a sokoto a shekara ta (1979) a gaban mai
alfarma sakin Musulmi Abubakar na Uku, an sake yi bayan shekaru biyar a Yankari ta jihar Bauchi
a shekarar (1983) a gaban Mai Martaba shehun Borno Alhaji Mustapha Umar El-Kanemi, inda aka sake cinma matsaya a
tsakanin malamai, wanda har aka kai gaban shugaban kasa Alhaji shehu
shagari ya albarkaci lamarin.
Hakanan Malamai sun sake zama don jaddada wannan
ittifaki, a shekarar (1988) a garin Kaduna
a gaban Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero. Ga wani yanki na jawabin
bayan taron:
a ci gaba ..
ReplyDeleteALLAH YA SHIRYE SHARIFF SALEH YA DAINA WANNAN MUMUNAR AQEEDAH TA SUFAYE
ReplyDeleteIdan ya bari, toya koma wace?
DeleteEnter your comment..allah yajaa zamaninka kuci gabada warware mana gaskiya.
ReplyDelete