Friday, May 31, 2013
Tushen Wahabiyanci a Nageria littafi na (Bakwai)
Tsokaci ne akan shahararren hadisin da Wahabiyawa suka rikeshi makami na raba kan al'ummar Annabi (SAW). Hadisin rarrabuwar al'umma zuwa kashi 73.
Shin ko kun san cewa hadisin nan bai inganta ba?
Ko kun san cewa Wahabiyawa sun makale masa ne don su sami kafa da daman kai musulmi wuta?
Za muga yadda aka 'fede biri har wutsiya' aka warware mana illolin da ke cikin Isnadi, da matanin Hadisin.
Ka hanzarta ka nemi kofin ka ka karanta!
Abuja:
07036200422
Kaduna:
08032060894
Kano:
08069752002
Friday, August 17, 2012
Shin Hadisan da Wahabiyawa ke yawan kafa hujja da su sun inganta? (1)
MATASHIYA
Wannan matashiya
kamar shimfida ne kafin mu shiga cikin maudu’inmu, na Magana a kan hukuncin yin bukin maulidin Annabi
Muhammadu (SAW) a shari’ar musulunci.
Ganin cewa duk
lokacin da masu fada da maulidi suka tashi yin sukarsu, babban makaminsu shine
Hadisan da suke yin hani ga aikata Bidi’a ko wani sabon abu, ko da kuwa abin
zai taimaka a wurin fahimtar musulunci, ko yaduwarsa, babu ruwansu in dai
Annabi (SAW) bai yiba, sshabbai basu yiba, to yinsa batane, sabo da haka
naga zaifi kyau mu yi nazarin wasu Hadisai guda biyu, wadanda aka fi dogara
dasu, a wajen kafa hujja.
Hadisan sune wadanda
Imamu Nawawiy ya kawosu a cikin littafinsa na Arba’una Hadisan, sune Hadisi na
biyar (5) da Hadisi na Ashirin da takwas (28) wadanda shima ya ciro sune a
cikin wasu littafan Hadisai.
Hadisi na farko
Wanda za mu fara magana
a kai shine Hadisi na biyar a cikin littafin arba’un nawawiy, wanda ya ciro a
cikin littafin sahihul Buhari da sahihul Muslim, ga abin da nassin hadisin yake cewa:
الحديث
الخامس:
عن أمّ
المؤمنين –أم عبد الله- عائشة رضي الله عنها، قالت: قال رسول الله صلى الله عليه
وسلم: "من أحدث في أمرنا هذا ما ليس منه فهو ردّ" رواه البخاري ومسلم،
وفي رواية لمسلم: "من عمل عملاً ليس عليه أمرنا فهو رد".
Ga yadda malam Abubakar Gumi ya fassara wannan
Hadisi, a littafinsa da ya fassara Arba’un Nawawiy da hausa:
“An karbo daga
Uwar Muminai Ummu Abdullahi A’ishatu (Yardan Allah ta tabbata a gareta) ta ce:
Manzon Allah “tsira da amincin sutabbata a gareshi” ya ce: wanda ya qago wani
abu da babu shi cikin al’amarinmu (Addini) to ba za a karba masa ba” Buhari da
Muslim suka ruwaito shi, A wata ruwayar
kuma ta Muslimu ya ce: “wanda ya yi wani aiki da baya cikin ummurninmu, to
aikin ya zama ba karbabbeba”.
Wannan hadisin
kamar yadda mu ka ce yana daya daga cikin manyan hujjojin masu da’awar yaqi da
bidi’a, wadanda suka ce yin taron maulidi yana daya daga ciki.
to da
shike yana daga cikin abinda yakan taimaka wajen fahimtar ma’anar hadisi shine a
sami sharhin da manyan malamai magabata sukaima hadisin, da sanin dalilin da ya
sanya aka same shi, ko daga wurin Ma’aiki (SAW) ko daga wurin wani
sahabi, kamar yadda sanin (asababun nuzuli) yake taimakawa a wurin fahimtar
Alqur’ani mai girma, don haka zamu koma cikin manyan littafai muga wane haske
za mu samu a game da wannan hadisin.
a)
fathul Bari
sharhin Sahihul Buhari:
A cikin wannan
littafi a mujalladi na (5) bugu na (دار المنار)
wanda Bin Baz da Al-baihaq, sukai masa ta’aliqI a ciki, a shafi na (336) a
kitabus sulhi (كتاب الصلح) littafin yin
sulhu, a cikin (باب إذا صلحوا على صلح جور فالصلح مردود)
ma’ana: Babin da yake cewa: “Idan aka yi sulhu, a sulhun da fin qarfi, to
wannan sulhun abin warwarewa ne”, a wajen wannan Magana ne aka kawo wannan
hadisi sabo da akafa hujja da shi.
A dangane da
inganci wannan hadisi, ba sai an bincika ba tunda ya zo a cikin sahihaini na
Buhari da Muslim, duk kuwa da cewa har a suma akan sami hadisan da basu inganta
ba, amma wannan hadisi malamai sun ingantashi, duk da cewa sayyidatuna A’isha (R.A)
ita kadai ta ruwaito shi a cikin sahabbai, sai dai wadanda suka ruwaito a wurinta
suna da yawa don haka ya zama hadisi mashahuri.
A cikin sharhin na
fathul-Bari an yi cikakken bayani na dalilin ruwaito wannan hadisi, a inda aka
ce ana batu ne a game da mutumin daya bayar da wasiya a game da dukiyarsa, sai
wasiyar tasa ta sabama nassin da ya raba wa magada abin da kowa zai samu, sai
aka nuna cewa wasiyar tasa ta zama (محدثات)
sai aka kawo wannan hadisi aka kafa hujja da shi, ga dai abin da Imam Asqalaniy
ya yi qarin bayani da shi:
"فيحج- بهذا الحديث- في إبطال جميع المنهية، وعدم وجود
ثمراتها المرتبة عليها، وفيه رد المحدثات، وإن النهي يقضي الفساد، لأن المنهيات
كلها ليس من أمر الدّين فيجب ردها، ويستفاد منه أن حكم الحاكم لا يغير ما في باطن
الأمر لقوله: "ليس عليه أمرنا" والمراد به أمر الدين، وفيه إن الصلح
الفاسد منتقض، والمأخوذ عليه مستحق الرّد".
Ma’ana:
Ana yin hujja- da wannan hadisi-a wajen bata ko wani irin
qulli wanda aka hana, da rashin yarda a sami amfaninta wanda yake cikinta, haka
nan ana warware fararrun abubuwa, don cewa anhana yana nuna bacin abin, sabo da
dukan abin da aka hana, bashi a cikin abin da addini ya yi ummurni da shi, don haka ya zama wajibi a warware, haka nan
ana gane cewa hukuncin mai hukunci baya canja haqiqanin al’amari-wanda shari’a
ta tabbatar-sabo da cewa:”abin da bashi a cikin ummurnin mu”, abin nufi abin
daya shafi addini, a ciki mun fahimci cewa dukkanin sulhi batacce zaa
warwareshi, duk abin da aka karba zaa mayar da shi”.
Anan mun ga asalin
dalilin daya sanya a ka kafa hujja da hadisin a fahimtar (Salaf) inda aka nuna
cewa: Halasta abin da aka hana, ko hana abin da aka halasta, anan ake kafa
hujja da wannan hadisin, ba akan ko wani abu sabo ba.
Da ace akwai wani
nassi a {ur’ani ko a hadisi da ya ce kada ayi taron farin cikin kewayowar ranar
da aka haifi Ma’aiki (SAW) muka ce sai mun yi, da sai a rinqa kafa mana
hujja da wanan hadisin, to amma babu.
b)
Sharhin Sahihul Muslim:
A cikin sharhin
sahihul Muslim na Sheikh Shamsud Din Muhammadu bin Yusuf (R.A) wanda aka
kawoshi a taqaice a mujalladi na (3) juzu’i na (5) bugun (دار الفكر - بيروت)
a shafi na (132) ga abin da akace:
"قوله عليه السلام: (من أحدث) أي أتى بأمر جديد (في أمرنا
هذا) أي في ديننا عبر عن الدّين به تنبيها على أن الدّين هو أمرنا الذي نشتغل به
(ما ليس فيه) أي شيئاً لم يكن له سند ظاهر أو خفي من الكتاب والسنة (فهو رد) أي
الذي أحدثه مردود باطل.
وفي
التيسر: (من أحدث) أي أنشأ واخترع وأتى بأمر حديث من قبل نفسه (في أمرنا) أي دين
الإسلام (هذا) إشارة إلى جلالته ومزيد رفعته (ما ليس منه) أي رأياً ليس له في
الكتاب والسنة عاضد (فهو رد) أي مردود على فاعله لبطلانه).
Ma’ana:
Zancen Mai tsira da aminci cewa: “Wanda ya fari wani abu”
ma’ana: ya zo da wani sabon al’amari, “a cikin al’amarimu wannan” ma’ana: a
addininmu, an fadi cewa addini ne don fadakarwa da cewa addini shine lamarin da
muka fi shagalta da shi “a bin da bashi a ciki” ma’ana: wani abu da bashi da
madogara a bayyane ko boye a cikin littafin Allah ko a sunnan Ma’aiki (SAW)“to an bar masa” ma’ana: abin da ya fare shi an bar masa
kayansa, don batacce ne.
A wani sharhin na Attaisir: “wanda ya fari wani abu”
ma’ana: ya qagi ko ya qirqiri, ko ya zo da wani lamari sabo, da kansa: “a cikin
al’amarinmu” ma’ana: a cikin addinin musulunci, “wannan” da aka ce, an fadi don
girmama shine, da nuna daukakansa, “wanda ba shi a ciki” ma’ana: ya qirqiro shi
ne da ra’ayinsa, bashi da wani madogara a littafin Allah, da Sunnar Ma’aiki (SAW)
to “an bar masa kayansa” ma’ana: an barma wanda ya aikata kayansa-Allah bai karba
ba-sabo da bacinsa”.
Wannan shine
sharhin da mafiya yawan malamai na sunnah magabata na gari suka tafi a kai, a
bin da nake son mu yi tsokaci a game da wannan sharhi guda biyu shine:
Na daya: shine cewa da akayi abinda bashi da wani
dalili da za a dogara da shi a littafin Allah ko a sunnan Ma’aiki (SAW),
wanda za a iya ganin hukuncin a zahiri, ko kuma wanda sai malamai mujtahidai za
su iya gano hukuncin, ta bin qa’idojin da malamai suka ajiye na (Istinbadi).
Na biyu: shine hukuncin aikata abin da bashi da
madogara a {ur’ani ko Hadisi shine ba za
a karba ba, watau ba zai sami ladan aikin ba.
Idan muka lura da
nassin Hadisin da Sharhin da mafiya yawan malamai suka yi nada dana yanzu, akan
wadan nan fahimta suke tsayawa, to amma sai muka ga wasu malaman masu ra’ayin Wahabiyawa sun qiqiri wani sabon
fassara na wannan hadisi mai cewa: “duk wanda ya fari wani abu sabo a
musulunci, to kamar yace ke nan addini bai cika ba, ko ya ajiye
kansa a matsayin Manzo, don haka in musulmi ne ya kafirta” da irin wannan
mummanar fassara ake cewa masu Bukin maulidin Annabi Muhammadu (SAW) ‘yan
bidi’a ne, ‘yan wuta, mushirikai, kafirai, hujjar su itace sabon fassara da sukai ma wannan hadisi,
fassarar da babu inda zaka ganshi sai a cikin littaffansu, na wahabiyawa wanda
shekarunsa bai kai shekaru dari biyu a duniya ba.
Babu wani littafi
wanda akai sharhin wadan hadisi mai shekaru dari uku dake dauke da irin wannan
sharhi na fitar da musulmi cikin musulunci don ya kawo sabon wani abu a addini,
ko da kuwa bashi da dalili a shari’a, matuqar bai yi da’awan annabta ba, sabo
da haka a wurin mafi yawan musulmi (ما
ليس منه) shine: kafirta musulmi da qiyasi mummuna.
·
Sharhin Jumlar: (في أمرنا هذا)
Idan muka dauki
wannan jumla mai cewa: “a cikin wannan al’amari namu” malamai sun hadu akan
cewa: “Al’amarinmu addini ake nufi” har kuwa da malam Abubakar Gumi, haka ya fadi
a wajen yin fassarar wannan hadisi da Hausa a littafinsa.
Mas’ala ta addini
ana fahimtarta ta hanyoyin da dama wanda malamai suka samo dalilin dogara da su
-don a zartas da hukunci- daga cikin Al-qur’ani
da Hadisi.
Wadannan dalilai
malamai su kan
kira su da suna (مصادر التشريع) muna iya kiransu
“madogara a shari’a”, malamai na Usulul Fiqhu, wasu sukan kasa su kashi biyu:
Na farko sune wadanda
malaman sunna suka yarda dasu babu sabani: Al-kitabu, Assunan, Al’ijma’i, da {iyasi.
Na biyu sune wadanda
malaman sunna suka sami sabani akai, wato wasu sun yarda da wasu, wasu kuma
basu yarda da wasu ba, sune: Masalihur Mursalah, Al-Istihsan, Al-Istishab,
Al-Urfu, {aulu Sahabiyin, Shar’u man qablana, D.S.S.
A qa’ida ta
malaman musulunci mujtahidai, kafin mutum ya ce wani abu bashi a cikin
musulunci a saurare shi, sai idan ya san wadannan dalilai tukuna, domin malamai
na mazhaba gabadayansu sun yarda da kashi na farko, amma sunyi sabani a cikin
wasu kadan a kashi na biyu.
·
Hanyar gane
hukunci a nassi, ta wannan hanya:
Da akwai ka’idoji
masu yawa da malaman Usulul Fiqhu suka ajiye wanda ake bi don a gane hukunci
daga cikin nassin da ya zo a {ur’ani ko Hadisi, da shike suna da yawa, bari mu dauki
misali guda daya shine: (اللفظ باعتبار كيفية دلالته على المعنى)
ma’ana: “ana lura da lafazi ta irin haqiqanin dalalar da aka samu a cikinsa don
sanin hukunci”, malamai sun kasa shi kashi hudu:
1.
(Ibarar
Nassi)shine: hukuncin da ake fahimta daga zahirin Nassin daya zo a Al-qur’ani
ko a hadisi, wanda duk wanda ya san larabci idan ya karanta zai gane hukuncin.
2.
(Isharar Nassi)
shine: hukuncin da za a iya fahimtarsa ta Isharar da Nassin ya nuna,
3.
(Iqtida’un Nassi)
shine: hukuncin da ba za a fahimce shi ba sai an qaddara wani lafazi daga
wajensa sannan a fahimci hukuncin da nassin ya qunsa.
4.
(Dalalatun Nassi)
shine: wanda malamai suka kasashi kashi biyu:
a.
(Mafhumil Muwafaqa) shine: hukuncin ya fito qarara
wanda ya kan
hade da wanda ba a fadaba,
b.
(Mafhumil
Muhalafa) shine: hukuncin da ake ganoshi na akasin wanda aka fada, kamar idan
akace ka tashi tsaye, kenan an hana ka cigaba da zama.
Wadannan qa’idoji
suna daga cikin wadanda ake yin laakari da su wajen fahimtar nassin daya zo a
cikin Al-qur’ani mai girma ko hadisin Ma’aiki (SAW) wanda shike fanni ne
mai fadin a wajen yin istinbadin hukunce-hukunce, wanda ya zo a alqur’ani
da hadisi.
Ba ana dogara ne
da zahirin Nassi shi kadai ba, don saboda iya larabci a bayar da hukunci yin
haka shi yake kawo sabani a tsakanin malamai masana, da ‘yan qungiya, da ‘yan qala
qato, da shauransu.
·
Ayoyin da suke yin
Ishara da ayi Bukin Maulidi:
Idan muka bi qa’idojin
da malamai suka ajiye za mu sami ayoyi a cikin Al-qur’ani mai girma da Hadisan
Ma’aiki (SAW) masu yawa wadanda suke yin Ishara da a taru ayi farin
cikin haihuwar Ma’aiki (SAW) bari
mu dauki ayoyi biyu muyi nazari, kamar yanda malamai suka yi bayani.
1.
Aya ta farko:
Itace aya ta (58)
a cikin Suratul Yunusa, inda Allah Madaukakin Sarki yake cewa:
(قُلْ بِفَضْلِ اللّهِ وَبِرَحْمَتِهِ فَبِذَلِكَ فَلْيَفْرَحُواْ
هُوَ خَيْرٌ مِّمَّا يَجْمَعُونَ) سورة يونس، آية: 58
Ma’ana:
“Kace da falalar Allah da Rahamarsa,
sai suyi farin ciki shi yafi-alhairi-daga abin da suke taruwa”.
Da shike a cikin a
yar ba ace mana kaza da kaza sune falalar Allah ba, kaza da kaza sune: Rahamar
Allah, sai mu koma cikin wasu tafsirai muji wani qarin bayani sukayi a wajen
tafsirin ayar:
a.
Tafsirin Ibun Kasir:
A mujalladi na (2)
a shafi na (422) a bugu na madaba’ar (دار
الفكر) ga abin da yake cewa:
"أي بهذا الذي جاءهم من الله من الهدى ودين الحق فليفرحوا
فإنه أولى ما يفرحون به".
Ma’ana:
“Ai da wannan abin da ya zo masu daga
Allah na daga shiriya da addinin gaskiya, da shi ya fi kamata su yi farin
ciki”.
2. Tafsirul
Faharur Razi:
A mujalladi na tara (9) a shafi na (124) a bugu na (دار
الفكر) ga abin da yace:
"أما المفسرون فقالوا: فضل الله: الإسلام، ورحمته:
القرآن".
Ma’ana:
“Amma a wurin malaman tafsiri sunce:
Falalar Allah, shine: Musulunci, Rahamarsa kuwa shine: Al-qur’ani”.
Anan a bisa qa’ida
da muke magana a kai na malaman Usulul Fiqhu cewa da malaman tafsiri su kayi da
(عبارة
النص)
ana nufin abin da za a taru a yi farin cikin samuwarsu sune: Musulunci da Al-qur’ani
To ashe kuwa da (إشارة
النص)
za a iya taruwa ayi farin cikin samuwar wanda aka aiko shi da musuluncin da
kuma Alqur’ani, shine Annabi Muhammadu (SAW) domin babu yanda za ayi a
taru ayi farin cikin haihuwar Ma’aiki (SAW) ba tare da anyi farin cikin
samuwar musulunci ba tare da Alqur’ani, ko ayi farin cikin samuwarsu ba tare da
ani yi farin cikin haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) ba.
Wannan dalili shi
ya sanya malamai da yawa suke kafa hujja da ita na dalilin yin bukin maulidin
Annabi (SAW).
Cewa kuwa da
wasu-‘yan qungiya suke yi: “ai wannan aya tana cikin Alqur’ani tun a zamanin
Ma’aiki (S.A.W) da Sahabbansa da Tabi’ai (R.A) me ya sanya su basu yi bukin maulidi ba, ko an
fisu sanin qur’ani ne?
Amsar wannan
tambaya zamu iya samunta ne, idan ‘yan qungiya sun gaya mana dalilin da ya
sanya sahabbai ba su yi tafsiri da watan azumi ba, basu rubuta tafsiri da
larabci ba, ba suyi tarjmansa a cikin wani harshe ba, sabo da dukkanin wadannan
ayyuka na addini ana yin sune don neman lada, alhali babu wanda ya yisu a qarni
na daya, da na biyu, da na uku, me yasa mu muka qirqire su?
2.
Aya ta biyu:
Itace ayar da ta
zo a cikin suratun Nisa’i, aya ta (124) inda Allah madaukakin Sarki ya ke cewa:
(وَمَن يَعْمَلْ مِنَ الصَّالِحَاتَ مِن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَى وَهُوَ
مُؤْمِنٌ فَأُوْلَـئِكَ يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ وَلاَ يُظْلَمُونَ نَقِيرًا)سورة
النساء: آية: 124
Ma’ana:
“Duk wanda ya yi aiki daga ayyukan na qwarai na majine kuma
mace, matuqar dai shi muminine, to wadannan sune zasu shiga aljanna, ba tare da
an zaluncesu, ko da kwatankwacin zaren qwallo dabino ba”.
A wannan aya inda aka ce (من
الصلحات)
na daga ayyuka na qwarai, harafin (ال) da harafin (من) na ma’arifa, a qa’idan
da malam Usulul Fiqhu suka fadi shine ko wani dayansu na nuna (إستغراقية) ce, watau ya hada
ko wani irin aiki na alhairi, wanda al’ummar musulmi suka yi a zamanin su,
kamar yanda aka qirqiri bude taro ko biki da addu’a, da rufewa da shi, da karanta
alqur’ani lokacin bude taro, da tashin wasu suyi wa’azi a wurin taron, ana
yinsa a kowani taro na addini ayau, da wani irin yanayi wanda (Salaf) basu san shi
ba.
Amma a yau babu wani malamin da yake
yin inkarin cewa suna daga cikin (Salihati) ayyuka na gari.
Irin wadannan ayyuka na alhairi basu da
bambanci da wadan da ake yi a wurin tarurrukan na maulidi, misali a duk inda
aka taru a kan fara ne da yin du’ai da karanta Alqur’ani mai girma, da yin
zikiri, da salatin Annabi (SAW) da karantar da
tarihin rayuwar Annabi (SAW) da waqoqin yabon sa, da yinma juna nasiha,
da ciyarwa sabo da Allah, wannan shine abin da ake yi a wurin taron bukin
maulidin Annabi (SAW) babu kuwa wani zamani da ba ayi irin wadannan
ayyuka na Alhairi, a tarihi ba haka nan ko wadanda ba su yin bukin maulidi suna
yin wadannan ayyuka na alhairi a wajen wasu tarurruka da suke yi a zamanin nan,
kamar bukin kamala musabaqan karatun Alqur’ani, taron gan-gamin wa’azi na jiha da
na {asa, da taron qaddamar da asusun neman timako, da bukin ba da lambar girma,
irin wanda Mu’assasa ta Sarki Faisal ta yi a narar 08/03/1987 don liqa ma
Abubakar Gumi lambar girma, saboda gudunmuwar da suka ce ya bayar wajen yada
musulunci, irin wannan bayar da lambar girma, bamu da labarin anliqama wani
sahabi, ko Tabi’i, ko Tabi’ut Tabi’in. duk cikansu (من
أحدث
في أمرنا) ne, an qirqiresu ne a cikin addini
amma ‘yan qungiya bamu taba jin sunce wa masu yinsa ‘yan bidi’a ba, balle su
kafirta masu yi, da wadanda suka bayar da wadanda aka baiwa.
Kamar
yadda muka bayar da misali da ayoyi biyu, haka nan za a sami hadisai masu yawa
da za a iya yin Istinbadin hukuncin yin bukin maulidi a ciki, da ma ko wani
irin aiki na alhairi a cikin musulunci, wannan shine bayaninmu dangane da
hadisi na biyar wanda ya zo a cikin littafin Arba’una Nawawiy.Daga Tushen Wahabiyawa A Nigeria Littafi na Shida Hukuncin Maulidi
Monday, August 6, 2012
Hujjojin Tawassuli daga Hadisan Ma'aiki (SAW)
Hadisan Ma’aiki (SAW) waDanda suka tabbatar da mustahabbancin
yin tawassali da neman albarkan magabata.
Musulmi
ba shi da madogarar da ya fi Alqur’ani mai
girma, da Hadisin Manzon Allah (SAW)
a kan ko wace irin mas’ala ta shari’a, bayansu sai Ijma’i da qiyasi da shauran
masadir wadanda aka yi sa6ani a kai.
A
jawabinmu da ya gabata mun ga inda Allah Madaukakin sarki ya yi umurni da a yi
tawassuli zuwa ga reshi, a suratul Ma’idah aya ta (35) kuma mun ga wadanda ya
nuna tawassulinsu ba zai amfane masu yi ba zuwa ga Allah a Suratul Isra’i aya
ta (57) a duka ayoyin biyu mun kawo tafsirin wasu malamai a game da su.
A
game da Hadisai wadanda suke yin Magana a game da tawassuli da Ma’aiki (SAW)
a halin yana raye da bayan ya yi wafati, da yin tawassali da salihan bayin Allah,
suma a halin suna raye da bayan sun yi wafati, da neman albarkacinsu, da nau’o’in
su, duka wani lamari ne da za mu iya tabbatar da su da Hadisai ingattatu
mutawatirai, kamar yadda muka sha fadi cewa wadannan littafai na Tushen
Wahabiyanci a Nigeriya, ba mu buqatar su yi girma yadda mai karatu zai qosa,
don haka Hadisai kadan zamu kawo, wadanda malaman Hadisi suka tabbatar da
ingancinsu in Allah ya yarda.
A.
Tawassuli da Annabi Muhammadu (SAW).
Hadisai
ingantattu sun tabbatar da halascin yin tawassali da Ma’aiki (SAW)
ba tare da yin la’akari da cewa yana raye ne ko bayan ya yi wafati ne, hasali
ma Annabawa da yawa (A.S.) sun yi tawassali da shi kafin bayyanarsa.
1.
Hadisin Tawassalin Annabi Adam (A.S.)
da shi.
Shekh
Sayyid Muhammadu Al’alawiy, Almalikiy Alhusainy, daya daga cikin manyan Malaman
da suke karantarwa a masallacin Harami na garin Makka ya fada a cikin
littafinsa mai suna (مفاهيم يجب أن تصحح)
ma’anar sunan wannan littafi shine: “Nau’o’in fahimtar da suka zama wajibi a
kawo gyara a kansu”.
Daga
cikin fahimtar da akwai na inkarin yin tawassuli da Ma’aiki (SAW)
daga cikin Hadisan da wannan shaihun malami ya kafa hujja da shi na halascin
yin tawassuli da akwai Hadisin da Imamu Hakim (R.A.) ya ruwaito a cikin
littafinsa: (Al-Mustadarak) ga hadisin:
قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
لما اقترب آدم الخطيئة قال: يا رب أسألك بحق محمد لما غفرت لي، فقال الله: يا آدم
وكيف عرفت محمداً ولم أخلقه؟ قال: يا رب لأنك لما خلقتني بيدك ونفخت فيّ من روحك
رفعت رأسي فرأيت على قوائم العرش مكتوباً لا إله إلا الله محمد رسول الله، فعلمت أنك لم تضف إلى
اسمك إلا أحبّ الخلق إليك، فقال الله: صدقت يا آدم إنه لأحب الخلق إلي، ادعني بحقه
فقد غفرت لك ولولا محمد ما خلقتك".
أخرجه الحاكم في المستدرك وصححه،
ورواه الحافظ السيوطي في خصائص النبوة وصححه، ورواه البيهقي في دلائل النبوة وهو
لا يروي الموضوعات، وصححه أيضاً القسطلاني، والزرقاني في المواهب الدنية، والسبكي
في شفاء السقام.
Ma’ana:
“Manzon
Allah (SAW)ya ce: ya yin da
Adamu (A.S.) ya yi kuskuren – cin itaciya – ya ce: ya Ubangiji ina roqonka da
haqqin Muhammadu (SAW)da
ka gafarta mani? Sai Allah ya ce: ya kai Adam ya ya a ka yi ka san Muhammadu (SAW)
alhali ban riga na halicce shi ba? Sai – Adam (S.A.) ya ce: ya Ubangiji a
lokacin da ka halicce ni da hannunka ka hura mani rai daga ranka, sai na daga
kai na sama sai na ga ni a rubuce a kan turakun al’arshi “Lailaha illallahu
Muhammadur Rasulullah” sai na san lallai baka hada sunanka da wani sai na mafi
soyuwar halitta a wajenka, sai Allah ya ce: ka yi gaskiya ya Adam (A.S.) haqiqa
shi ne mafi soyuwar halitta a guna, tunda ka kirani da haqqinsa, don haka na
gafarta maka, saboda ba domin Muhammadu ba (SAW)
da ban halicce ka ba”.
Al-Hakim
ya fitar da wannan hadisi a cikin “Al-Mustadarak”, ya kuma tabbatar da
ingancinsa, Al-Hafiz Assuyudiy ya ruwaito shi a cikin “Khasa’isun Nubuwwa” ya
inganta shi, Al-Baihaqi ya ruwaito shi a cikin “Dala’ilun Nubuwwah” kuma an san
bai ruwaito – hadisai – mauduai, hakannan Al-Asqalani ya inganta shi , da
Az-Zarqani, a cikin “Al-Mawahibul Ladunniya” da As-Sabqi a cikin “Shifaus Siqam”.
Wannan
hadisi ingantacce ko da shi kadai muka samu ya isa a kafa hujja ga maqiya yin
tawassuli da Ma’aiki (SAW) wadanda
suka ce ba ayi sai da wanda yake raye, to sai gashi Annabi Adam (A.S.) ya yi
kamun qafa da shi kafin ma a halicce shi, balle kuma a ce yana raye, ko bayan
wafatinsa.
2.
Hadisin da Ma’aiki (SAW)
ya koyar da yadda za a yi tawassuli da shi:
Furofesa
Shekh Aliyu Jumah Mufti na qasar Masar ya amsa wata fatawa a game da yin
tawassuli da Annabi (SAW) a cikin littafinsa mai suna: (البيان لما يشغل الأذهان) Ma’ana: “Bayani a game da abubuwan da yake
Dau kan hankali” a wajen amsa fatawarsa a game da tawassuli ya kawo Hadisin da
aka kar6o daga Usman bin Hanifi cewa:
"أن
رجلاً ضرير
البصر
أتى النبي صلى الله عليه وسلم فقال: ادع الله لي أن يعافيني؟ قال: إن شئت دعوت وإن
شئت صبرت فهو خير لك، قال: فادعه. قال" فأمره أن يتوضأ فيحسن وضوءه ويدعو
بهذا الدعاء: "اللهم إني أسألك وأتوجه إليك بنبيك محمد نبي الرحمة، يا محمد
إني توجهت بك إلى ربي في حاجتي هذه لتقضي لي، اللهم فشفعه فيّ".
أخرجه
أحمد في مسنده، والترمذي في سننه، وقال هذا حديث حسن صحيح، والنسائي في الكبرى،
وفي عمل اليوم والليلة، وابن ماجه في سننه، والحاكم في المستدرك.
(قال الدكتور) ولا نعلم أحداً ضعفه
حتى في ذلك العصر الحديث ممن اشتهر بالمنهج التشديدي، فقد صححه الشيخ الألباني،
فليس هناك من يعترض على سند الحديث ولا متنه.
Ma’ana:
“Wani
mutum da ba ya gani sosai ya tafi wajen Annabi (SAW)
sai ya ce masa: ka roqan mani Allah ya bani lafiya, sai yace: in ka so zan roqan
maka Allah, in ka so kuma ka yi haquri ya fi maka alhairi, sai ya ce: ka roqe
shi, sai Manzon Allah (SAW)
ya ummurce shi da ya yi Al-walla, ya kuma kyautata alwallar, ya yi du’ai da
wannan addu’ar: ya Allah ina roqonka ina kuma fuskantarka da alfarmar Manzaon ka
Muhammadu Annabin rahma, ya Muhammadu ina fuskantarka da alfarmarka zuwa waje
Ubangijina a game da buqata ta wannan, ya Allah ka sanya cetonsa a gareni”.
Imamu
Ahmad ya fitar da wannan hadisin a Musnad Dinsa, da Tirmizi a sunan Dinsa ya kuma ce hadisi ne mai kyau, kuma
ingantacce ne, da An-nasa’i a cikin Al-Kubra, da kuma Amalil – yam-Wallailih,
da Ibin Majah a cikin sunan Dinsa da Hakim a cikin Al-Mustadrak.
(Babban
Malami Dr. Aliyu Juma) ya ce: ba mu san wani wanda ya raunana wannan hadisin
ba, har a wannan zamanin daga cikin waDanda suka yi fice wajen yin tsanani a
manhajarsu, har da Shaihu Al-Albaniy ya inganta wannan hadisi, hasali babu wani
da aka samu ya soki masu ruwaito shi, ko ya soki mataninsa.
Idan
muka lura da wannan hadisi ingantacce, za mu ga Ma’aiki (SAW)
ne da kanshi yake karantar da yadda za a yi kamun qafa da shi a wurin Allah,
domin kai wa ga biyan buqata, don haka wani Dan Bidi’an zai zo bayansa da
shaikaru Dari bakwai, ya ce mana ba a yin kamun qafa da shi mu saurare shi?
3.
Hadisin yin Tawassuli da Ma’aiki (SAW)
bayan wafatinsa:
Shaihul
Azhar (Rahimahul lahu) Jadul-Haq Aliyu Jadul-Haq ya tabbatar da mustahabbancin
yin tawassuli da Annabi (SAW) bayan wafatinsa, a
cikin littafinsa mai suna(بيان
للناس) da Hadisin da Imamu Al-Baihaqi ya ruwaito mai cewa:
" روي البيهقي في " دلائل
النبوة" أن قحطاً أصاب الناس في زمن عمر، فجاء رجل قبر النبي صلى الله عليه
وسلم فقال: يا رسول الله، استسق الله لأمتك فإنهم قد هلكوا، فأتاه الرسول في
المنام، فقال: ائت عمر فاقرئه السلام واخبره أنهم مسقون، وقل له: "عليك الكيس
الكيس" فأتى الرجل عمر فأخبره فبكى، وقال: يا رب ما آلو إلا ما عجزت عنه،
يعني لا أقصر إلا فيما عجزت عنه".
قال شيخ
الأزهر: (في الحاشية) اسناده صحيح كما قال ابن كثير في البداية، وروي مثله ابن أبي
شيبة، وقال ابن حجر في فتح الباري: "اسناده صحيح".
Ma’ana:
Al-Baihaqi ya ruwaito
a (Dala’ilun -Nubuwa) cewa: Fari ya aukawa mutane a zamanin sayyadina Umar
(R.A.) sai wani mutum ya zo qabarin Annabi (S.A.W) ya ce: ya Manzon Allah ka roqi
Allah ya shayar da al-ummarka, saboda sun hallaka, sai Manzon Allah (SAW) ya zo ma-wannan
mutumin-a mafarki ya ce ma shi je ka wajen Umar ka yi masa sallama sannan kuma
ka ba shi labari cewa za a shayar da su ruwan sama, kuma ka faDa ma shi cewa:
“Ina horonka da matuqar hankalta” sai mutumin –da ya farka- ya je wajen Umar
(R.A.) ya ba shi labarin, sai Umar ya fashe da kuka, ya ce: ya Ubangiji ba zan taqaitaba sai inda qarfina
ya qare, Ma’ana ban taqaituba, sai a cikin abin da na gajiya ga yinsa”.
Shaihul
Azhar (R.A.) ya faDi a Hashiya cewa Isnadin – wannan Hadisi – ingantacce ne
kamar yadda Ibun Kasir ya faDa a cikin Al-Bidaya, kamar yadda Ibni Abi Shaibata
ya ruwaito kwatankwacinsa, Ibnu Hajar ya faDa a cikin Fatahul- Bari cewa:
Isnadinsa ingantacce ne.
Hadisai
ingantattu a littatafan Hadisai masu yawa, sun ba mu labarin cewa a lokacin da
Ma’aiki (SAW) yake raye idan an sami fari an sha
zuwa ana kama qafa da shi ya roqi Allah a sami ruwa, don saboda kar a zaci cewa
bayan wafatinsa ba shi da wani tasiri, saboda haka wannan bawan Allah wanda ya
yi imani da cewa Ma’aiki (S.A.W) a cikin qabari yana roqan Allah ya amsa kamar
yadda yake mayar da sallama ga duk wanda ya yi masa, sai ya tafi ya yi kamun qafa
da shi, Khalifansa na biyu sayyadina Umar (R.A.) wanda abin ya faru a
zamaninsa, bai qaryata ba sabo da sanin matsayin Ma’aiki (SAW) hasali
na dama ma ya yi da cewa shi ya kamata a ce ya yi haka.
Wannan
hujja ne mai gamsarwa da take tabbatar da neman du’ain Ma’aiki (SAW)
don yayewar wani bala’i a tsakanin al’ummarsa, ‘ya Rasulullahi, muna kamun qafa
da kai zuwa ga Allah ya shiriyi musulmi masu tauye maka haqqi’, ako ina suke.
4.
Hadisin yin Tawassuli da Ma’aiki (SAW)
a ranar gobe {iyama:
Imamu
Buhari da Imamu Muslim da Imamu Trimizi da Imamu Ibin Majah da Imamu Darami
Allah ya yarda da su duk cikansu sun ruwaito wannan hadisi mai tsawo na yin
tawassuli da Ma’aiki (SAW) a ranar tashin qiyama.
Ga
abin da Imamu Buhari ya ruwaito a
Kitabul Fathul Bari sharhin Sahihul Buhari Mujalladi na (13) shafi na (573)
bugun: “Darul Manar”
عن
أنس أن النبي صلى الله عليه وسلم قال: يجمع الله المؤمنين يوم القيامة فيقولون: لو
استشفعنا إلى ربنا حتى يريحنا من مكاننا هذا، فيأتون آدم فيقولون: يا آدم أما ترى
الناس؟ خلقك الله بيده، واسجد لك ملائكته، وعلمك أسماء كل شيء، اشفع لنا إلى ربك
حتى يريحنا من مكاننا هذا فيقول: لست هناك – ويذكر لهم الخطيئة التي أصاب – ولكن
ائتوا نوحاً فإنه أول رسول بعثه الله إلى أهل الأرض، فيأتون نوحاً فيقول: لست هناك
– ويذكر خطيئة التى أصاب، ولكن ائتوا إبراهيم خليل الرحمن، فيأتون إبراهيم فيقول:
لست هناكم – ويذكر لهم خطايه التي أصابها – ولكن ائتوا موسى عبداً أتاه الله
التوراة وكلّمه تكليماً، فيأتون موسى موسى فيقول: لست هناكم – ويذكر لهم الخطيئة
التي أصابها – ولكن ائتوا عيسى عبد الله ورسوله وكلمته وروحه، فيأتون عيسى فيقول:
لست هناكم، ولكن ائتوا محمد صلى الله عليه وسلم عبداً غفر له ما تقدم من ذنبه وما
تأخر، فيأتونني، فأنطلق، فاستأذن على ربي فيؤذن لي عليه، فإذا رأيت ربي وقعت له
ساجداً، فيدعني ما شاء الله أن يدعني، ثم يقال لي: ارفع محمد قل يسمع، وسل تعطه،
واشفع تشفع، فأحمد ربي بمحامد علمنيها، ثم أشفع.........
Ma’ana:
An karbo daga Anas (R.A.)
cewa Ma’aiki (SAW)ya ce:A ranar Al-qiyama, Allah yakan tara-hankalin – muminai sai su
ce: me zai san ya ba za mu yi kamun qafa ba zuwa ga Ubangijin mu, don ya hutar
damu daga wannan hali da muke ciki, sai su tafi wurin Adam (A.S.) su ce masa:
ya Adamu baka ganin halin da mutane suke ciki? Kai ne fa Allah ya halicceka da hannunsa
- ba Uwa ba Uba mala’iku suka yi
ma sujjada, - Allah – ya sanar da kai sunan komi da komi, kayi mana ceto mana a
wurin Ubangijinka domin ya hutar damu daga wannan hali da muke ciki – na dogon
tsayuwa da a zaba- sai – Adam (A.S) – ya ce: ai bani da ikon yin haka – ya faDa
masu kuskuren day a yi (na cin itaciya) – sai dai ku tafi wurin Nuhu (A.S.)
wanda shine farkon Manzo da Allah ya aiko a bayan qasa, sai – Jamaa – su tafi
wurin Nuhu (A.S.) – su faDa masa abin da
yake tafe da su – sai ya ce: bani da iko – ya gaya ma su kuskuren da ya aikata
(na roqon Allah ya hallaka al’ummarsa waDanda suka qi binsa) amma ku tafi wurin
Ibrahim maji daDin Ubangiji, sai su tafi wurin Ibrahim (A.S.) – su gaya masa buqa
tarsu – sai ya ce: bani da iko – ya gaya masu wasu kurakurai da ya aikata (na
yin qarya don karantarwa) sai dai ku tafi wurin Musa (A.S.) wanda bawane wanda
Allah ya ba shi littafin attaura, ya kuma yi zance da shi, sai su tafi wurin Musa
(A.S.) – su faDa masa
abin da yake tafe dasu – sai ya ce: bani da iko- ya faDa masu kura kuren da ya
aikata (a wurin ceto da yin gwaninta) sai ya ce: masu amma ku tafi wurin Isah
bawan Allah Manzonsa, Kalmarsa, Ruhinsa, sai su taho wurin Isah (A.S.) sai ya
ce: masu bani da iko, sai dai ku tafi wurin Muhammadu (SAW)wanda shi bawane da
Allah ya gafarta masa zunubansa gabaki Daya, sai su taho wuri na- su faDa mani
buqatun su – sai na tafi na nemi izinin saduwa da Ubangijina, sai ya bani
izini, sai na ga Ubangijina, sai na faDi na yi masa sujjada, sai ya ajiyeni a
inda ya so ajiyeni, saannan ya ce mani Daga kai Muhammadu, ka faDi a saurareka,
ka tambayi – abin da ka keso- a ba ka, ka nemi ceto a baka ceto, sai na yabi
Ubangijina da duk wani yabo da ya sanar dani, saannan sai na yi ceto…………
Wannan
hadisi mai tsawo, wanda duk malaman hadisi sun inganta shi, dukanin alummar
musulmi a duk inda suke a doniya, sun yarda da cewa Annabi Muhammadu (SAW)
zai nemi a bashi ceto a ranar tashin al-qiyama wanda ake kira (الشفاعة العظمى) kuma Allah MaDaukakin Sarki zai bashi,
wannan ceto har Wahabiyawa na Saudiya sun yarda da a kwaita, amma abin mamaki a
nan qasar tamu ta Najeriya sai da aka sami wasu 6angare na ‘yan Izala almajiran
malam Abubakar Gumi, waDan da suka fito suka qaryata batun yin kowane irin ceto
a ranar qiyama, a yayin da aka sami wasu kuma suna tabbatar da cewa da akwai
ceto a Lahira suka dosa kiran taro ya su - ya su kan wannan mas’ala suna
kafirta juna, har sai da magana ta kai gaban Malam.
A
jaridar Gaskiya tafi kwabo ta ranar Asabar (24) ga watan Nuwanba, 1991 bugu ta
(5,125) a shafi na farko- mai Dauke da hoton Malam Abubakar Gumi – ga abin da
aka rubuta: “DUK WANDA YA CE BA CETO KO AZABAR
{ABARI YA YI RIDDA in ji Gumi”.
Idan
ana neman qarin bayani sai a nemi wannan jarida a karanta, zaa ga inda malamin
ya tabbatar da cewa za a yi Tawassuli da Ma’aiki (SAW)
a ranar qiyama, kuma a bashi, haka nan yace ana baiwa Annabawa da Mala’iku, da Waliyyai
ceto a wannan ranar, idan Allah ya yi masu izini.
Amma
bari kuji irin martanin da wani babban almajirinsa na biyu a majalisar tasa,
irin amsar da ya bayar da aka tambayeshi a game da wannan jawabi na malamin
nasa:
Tambaya: Maganar
ceto shin me ya sa mutane su ke damuwa a kanta?
Amsa: “Masu neman ceton nan su aka aiko ma
Annabawa don su faDa masu, maganar ceton nan, mu mun yi imani Allah kaDaine me
ceto kuma ceton nan ga hannun Allah yake, kuma Allah yana ceton wanda ya so,
daga cikin rahamanshi, amma cewa wasu mutane za su yi ceto, ko Annabawa za su
yi ceto da sauransu dai to waDan nan maganganune wanda mushurikai sun ka faDi
tun da daDewa, maganganune na mushurikai suke biyan wasu masu cewa, don haka
cewa akwai wasu masu ceto, to ga addinin musulunci ya nuna mana babu wani mai
ceto sai Allah, maganan ceto Dinnan dama can mushurikai ana faDa dasu akan
ceto, don haka duk wanda kaji ya shake fuska ya shake murya yana cewa a kwai
ceto, zaa yi ceto, to jinin mushurikai yake yawo cikin jikin shi, ceton nan
babu wanda kayi nai sai Allah….)
muna da cikakken wannan bayani a kaset
na firarrakin da aka yi da wannan malami almajirin Abubakar Gumi, koda shike
daga baya ya ce shi ba almajinrinsa bane da karatunsa Gumi ya ganshi.
Daga
wannan jawabi nasa zamu fahimci shima Abubakar Gumin ya zama mushuriki don haka
shi ma gara Kirista da shi, kamar yadda ya ce: “Gara Kirista da dan dariqa” don
ya yarda da ceto a lahira, inji
almajirinshi.
B.
Tawassuli da Bayin Allah nagari:
Kamar
yadda mu ka kawo hadisai ingantattu masu yawa waDanda suka tabbatar da yin
tawassuli da Ma’aiki (SAW) tun kafin ya fito duniya, ta yadda
Annabawa da ban- da ban suka rinqa yin kamun qafa da shi a wurin Allah, kuma
Allah ya sauraresu ya biya masu buqata, haka nan za muga hadisai ingantattu da
suka tabbatar da yin tawassuli da shi yana raye da tun kafin ya zama Manzo, da
bayan ya zama Manzon Allah (SAW) hadisan da har dan Taimiyya
ya yarda dasu, inda aka sami sa6ani a hadisan yin tawassuli da shi bayan ya yi
wafati waDanda malamai masu yawa sun tabbatar da ingancin su fanDarewar sa da
na mabiyan sa, ba zai dame mu ba.
A
wannan babi zamu dubane, ko suma Salihan Bayi zaa iya yin tawassuli dasu kamar
yadda aka yi da Ma’aiki (SAW) a halin suna raye da
bayan sun yi wafati, sabo da kasancewarsu khalifofinsa ko magadansa, zai yiwu a
yi kamun qafa dasu, a halin suna raye da bayan sun yi wafati?
1.
Hadisin da ya yi umurni da ayi
tawassuli da wani bawan Allah idan ya bayyana:
Uwaisul
qarni wanda shi ba Sahabibane Tabi’ine, amma
sai ga shi Ma’aiki (SAW) ya na ummurtan Sahabai harma da waDanda
aka yi masu bishara da shiga Aljanna, da cewa idan sun sadu da shi su yi
tawassuli da shi ta neman ya yi masu du’ai, ga dai abin da hadisin yake cewa:
عن
أُسير بن جابر قال كان عمر بن الخطاب إذا أتى عليه أمداد أهل اليمن سألهم أفيكم
أويس بن عامر؟ حتى أتى على أويس، فقال: أنت أويس بن عامر؟ قال: نعم، قال: من مراد
ثم من قرن؟ قال: نعم، قال: فكان بك برص فبرأت منه إلا موضع درهم؟ قال: نعم، قال:
لك والدة؟ قال: نعم، قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: يأتي عليكم
أويس بن عامر مع امداد أهل اليمن من مراد ثم من قرن كان به برص فبرأ منه إلا موضع
درهم له والدة بها بر لو أقسم على الله لأبرّه فإن استطعت أن يستغفر لك فافعل
فاستغفر لي فاستغفر له".
رواه مسلم في كتاب فضائل الصحابة، باب من فضائل أويس القرني
رضي الله عنه.
Ma’ana:
“An
kar6o daga Usairu Dan Jabir ya ce: Umar Dan KhaDDabi (R.A.) ya kasance ya na
tambayar gungun mutane Yaman- in sun zo – a cikinku da a kwai Uwaisu Dan amir?
Har zuwa lokacin daya haDu da Uwaisu, sai ya tambaye shi ya ce: kaine Uwaisu Dan
Amir? Ya ce: na’am, ya ce: daga murad? Sannan kuma daga qarnu? Ya ce: na’am,
sai ya ce: da ka zama kana da kuturta, sai ka warke, sai Dan wurin da bai wuce
faDin dirhamiba, ya ce: na’am, sai ya ce: kana da mahaifiya? Ya ce: na’am, sai
– sayadina Umar – ya ce: naji Ma’aiki (SAW)yana
cewa: Uwaisu Dan Amiru zai zo maku tare da wata tawagar mutanen Yamen daga
murad, sannan daga qarnu, ya kasance yana da cutar kuturta sai ya warke sai Dan
wani wuri mai faDin dirhami, ya na da mahaifiya wanda yake mata biyayya, da zai
rantse akan Allah – zai yi wani abu – ba zai bashi kunyaba, idan – mutun- ya
sami ikon neman ya roqa maka gafara ka nema, - don haka – ka roqamani gafara,
sai ya roqa masa”.
Imamu
Muslim ya ruwaito wannan hadisi a littafin falalar Sahabai, a cikin Babin
falalar Uwaisul-qarni (R.A.)
Wannan
hadisi idan muka koma ka’ida ta Usulul-Fiqh, bayan ya tabbatar mana da halascin
yin tawassuli da bawan Allah na gari don samun albarka du’ainsa, a wajen
isharar nassin zaa fahimci a bubuwa da yawa:
·
Tabbatar da cewa Ma’aiki (SAW)
ya san gaibi don gashi ya bayar da labarin zuwan mutumin da ba su yi zamani
tare da shi ba, babu shakka mai Ishiriniya ya faDi gaskiya a inda yake cewa:
بصير بسر
الغيب قبــــل كيانه * له يقرب المرمى وترتفع الحجب
Ma’ana:
Ma’aiki
(SAW)masanine na asirin da
yake 6oye kafin ya bayyana.
Da
shi ne ake kusantan abin guri, sa’annan akawar da ko wane irin shamakai.
·
Hakanan mun fahimci cewa zaa iya samun
bayin da Allah ya yarda dasu a ko wace
irin jinsi na mutane, kuma a ko wani zamani kamar yadda Ma’aiki (SAW)
ya ke cewa:
"مثل أمتي مثل
المطر لا يدري أوله خير أم آخره"
Ma’ana:
“Kwatankwacin
Alummata kamar ruwan samane, baa saniba na farkone yake Dauke da alhairi, ko na
qarshensa”, Imamu Tirmizi ya ruwaito wannan hadisi.
·
Hakanan zamu fahimci cewa daga cikin
abin da ya kai shi ga samun wannan matsayi shine biyayya ga mahaifiya “bai kasance a cikin irin mutanen da
sukan sayi qwaryar Nono su kai mataba, don su biya ta nonon da ta shayar
dasu domin kada tayi masu gori”.
·
Har ila yau muna iya fahimtar cewa
wannan hadisi maida martanine ga masu cewa sun fi qarfin su sanya wani malami
ya roqa masu Allah, don ba a fisu kusa das hi ba, kamar yadda muka ji ana fira
da wani Tsohon mai sarauta Dan Izala a kafan watsa labarai yana yin al-fahari
da cewa shi bai sanya wani malami ya roqa masa Allah – Allah ya shiryeshi – shi
bai san har Ma’aiki (SAW) ya gayama Sayyadina Umar (R.A) lokacin
da zai je umra cewa:"لا
تنسانا يا أخي من دعائك" Ma’ana: “Kar ka manta damu cikin du’ainka
ya Dan Uwa”.
2.
Hadisin da akai kamun qafa da Abbas
(R.A.):
An
sami hadisai ingantattu masu yawa waDanda suka tabbatar da cewa sau da yawa
idan an sami fari (rashin ruwa) a kan zo a yi kamun qafa da Ma’aiki (SAW)
zuwa ga Allah domin samun ruwa, sabo da kar a zaci yin haka ya ke6anta ne kawai
da shi Ma’aiki (SAW) sai Sayyadina Umar (R.A) a lokacin
Khalifancinsa da aka sami fari, Sabo da kar a zaci cewa sabo da Manzon Allah (SAW)
ya yi wafati babu shauran yin kamun qafa da wani, sai ya yi tawassuli da
sayyadina Abbas (R.A) qanin mahafin Ma’aiki (SAW)
don a sami ruwa.
Ga
hadisin da Imamu Buhari (R.A) ya ruwaito a sahihinsa a kitabul Istiqa’i:
"عن
عمر بن الخطاب رضي الله عنه أنه إذا اقحطوا استسقى بالعباس بن عبد المطلب رضي الله
عنه فقال: اللهم إنا كنا نتوسل عليك بنبينا فتسقينا وإنا نتوسل إليك بعمّ نبينا
فاسقنا، قال: فيسقون".
Ma’ana:
“An kar6o daga Umar Dan
Khaddab (R.A) ya na cewa: Idan an yi mana fari mukan nemi-Allah ya shayar damu-
da Abbas Dan Abdul Muddalib (R.A) sai yace: Ya Allah mun zama muna masu yin
tawassuli zuwa gareka da Annabinmu kana shayar damu, ayau muna masu yin
tawassuli zuwa ga reka da qanin Mahaifin Annabi (SAW)ka shayar damu, sai
yace: sai a ka shayar da su”.
Wannan
hadisi ingantacce wanda Imamu Buhari ya ruwaito a sahihin littafinsa ko shi kadai
ya isa ya tabbatar mana da cewa ana yin tawassuli da wani bawa na Allah, ya na
rayene ko bayan ya yi wafati, wasu su kance ai dama sun yarda idan mutum ya na
raye za a iya yin kamun qafa dashi zuwa ga Allah amma idan ya rasu ne ba’a yi
sabo da wannan hadisi.
Malamai
da yawa sun yi raddi a game da wannan mummunar fahimtar domin ai Allah a ke roqo
ya yi abin sabo da matsayin wani bawa nasa, a wurin shi, tawassuli da du’ain
wani bawan Allah ne sai idan yana raye ne za ka nema ya yi maka.
Sabo
da wadannan dalilia da muka samu daga dan Khaddabi (R.A) da tawassulinsa da
Uwaisul qarni, da tawassulinsa da Abbas (R.A) bai kamata mu barsu don maganar dan
Taimiyya ko dan Abdul-Wahab ba, ko dan Mahmud Gumi ba.
3.
Hadisin yin Tawassuli da duk wani mai
roqon Allah:
Saboda
Ma’aiki (SAW) ya nuna mana cewa babin wadan da ake
yin tawassuli dasu abune mai fadi, sai shi da kansa ya koyar da yin tawassuli
da wasu bayin Allah.
Imamu
Ibin Majah ya ruwaito wani hadisi a cikin sunnarsa a babin (المشي إلى الصلاة) Tafiya zuwa Masallaci, wanda yake cewa:
"عن
أبي سعيد الخدري قال: قال رسول الله صلى الله عنه وسلم: من خرج من بيته إلى الصلاة
فقال: اللهم إني أسألك بحق السائلين عليك، وأسألك بحق ممشاي هذا فإني لم أخرج
أشراً ولا بطراً ولا رياءً ولا سمعة وخرجت اتقاء سخطك وابتغاء مرضاتك فأسألك أن
تعيذني من النار، وأن تغفر لي ذنوبي إنه لا يغفر الذنوب إلا أنت، أقبل الله عليه
بوجهه واستغفر له ألف ملك".
Ma’ana:
An
kar6o daga Abu Saidul- Khudri ya ce: Manzon Allah (SAW)ya
ce: wanda ya fita daga gidansa zuwa masallaci sai yace: Ya Allah ni ina mai roqonka
don alfarman masu roqonka da kuma alfarmar tako na wannan, domin banfito don
sharri ba, ko don girman kai ba, ko sabo da riya, ko don Jida kai, na fitone
don tsoron hushinka, da neman yardanka, ina mai roqonka ka tsamar dani daga
wuta, ka kuma gafarta mani zunubaina, domin babu wani mai gafartawan zunubi sai
kai, Allah zai fuskance shi da fuskarsa, kuma Mala’iku dubu za su neman masa
gafara”.
Wannan
hadisi yana tabbatar mana da cewa mustahabine ga musulmi ya yi tawassuli zuwa
ga Allah da duk wani bawan Allah mai roqon Allah a duk inda ya ke.
neman albarka da wasu ababe
na Ma’aiki (SAW)
Yana daga cikin sunna mai kyau a nemi albarkan Ma’aiki (SAW) da duk wani abu da ya ji6ince shi.
Sau da yawa mukan karanta a cikin littafai na Wahabiyawa,
kamar yadda mu kan ji ta bakin ‘yan qungiya suna cewa: neman albarka da wani
abu na Ma’aiki (S.A.W) ko na wani Salihin bawa Waliyyi, shirka ne domin kanuna
abin yana da tasiri kenan ba Allah ba a cewarsu.
Don mu nuna ma “‘yan Izala ‘yan bidi’a” cewa abin
ba haka bane, a wannan babi zamu kawo maku Hadisai, da bayanai waDan da suka
tabbatar da cewa sunnace a musulunci a nemi tubarraki da wani abu na Ma’aiki (SAW) da na wani Salihin bawa, kamar yadda ake yin tawassuli
da su don samun biyan buqata, Sahabbai (R.A) sune suka fara sai tabi’ai, sai tabiut
tabiina abin yacigaba harya kawo kanmu, ba mune ‘yan dariqa muka faraba,
sunnace wadda muka gada daga bayin Allah nagari, Salafus salih, ko da yake ku
salafus saleh a wajen ku shine Dan Taimiyya da almajiransa.
Subscribe to:
Posts (Atom)