Monday, July 30, 2012

Gabatarwa

Gabatarwa 

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki wanda yake cewa  ku yi riko da igiyar Allah gaba daya kada ku rarraba.

 Tsira da aminci su tabbata ga Shugabanmu Annabi muhammadu (S.A.W) wanda yake cewa: "Wanda ya ga abin ki daga cikin ku ya kawar da shi da hannunsa, idan ba zai iyaba ya yi da bakinsa, idan ba zai iyaba ya ki abin a Zuciyar sa wannan shi ne mafi raunin Imani".
Allah ya yarda da magabatan da suka tafi akan tafarkinsa madaidaici, da masu yin koyi das u har zuwa ranar tashin kiyama.
Bayan haka wannan takaitaccen bayani mai zuwa a cikin wannan (GABATARWA) littafi na faroko cikin jerin littafinmu mai suna: (TUSHEN WAHABIYANCI A NaJERIyA) wata karamar shimfida ce wacce za tayi wa mai karatu jagoranci zuwa ga wani sako wanda muke fata mai karanta wannan littafi ya fahimta daga karshe cewa "akwai wasu mutane da suke ta yunkuri wai sai wannan kasar ta rungumi akidar  Wahabiyanci a matsayin akidar ko wane musulmi kamar yadda abin yake a kasar Saudiyya" in ba haka ba kuwa ba sauran zaman lafiya.
A wajen kokarinmu na muyi ma 'yan'uwa musulmai takaitaccen bayani a rubuce, sai muka ga ya kamata mu faro bayani  tun daga farkon shirye-shiryen da aka fara gabatarwa a matsayin asasi na ginin wannan akida ta wahabiyanci don ganin ta ci gari da  yaki kama tun daga rubutun rahoto har zuwa fassara kur'ani, da buga littafai kanana da manya , da kafa kungiyoyi, da gangamin wa’azi kamar haka:
-          Rubuta kananan jawabai a jaridu kamar yadda yake a jaridar Gaskiya ta fi Kwabo da wasu jaridu na Hausa da Turanci.
-          Rahotanni na sakamakon bayan tarurruka.
-          Koyarwa ta hanyoyin sadarwa (Redio - Kaset na sauraro da na ji da gani).
-          Rubuta littafai, farawa tun daga rubuta kananan Makaloli har zuwa ga tafsiri, da sauran wasu littafai.
-          Kafa kungiyoyi da yin gangamin wa’azi daga gari zuwa gari.
Wadannan ginshikai guda hudu sune aka dogara da su wajen dora ginin akidar a kansu, kuma akan su ake so kowane musulmi ya dora nashi ginin. Ganin shirin nasu ya fara ne da rubuta kananan jawabai har zuwa fassara kur’ani da Hausa da Larabci da Turanci domin cimma manufa, ganin haka shine tarko mafi inganci wajen kama musulmi- kamar yadda bayani zai zo – shi ne muka ce bari mu sa mai karatu a hanya shima domin ya fara da abinda shirin samarma akidar Wahabiyyanci gindin zama ya fara, kafin mu ja mai karatu zuwa ga yin tsokaci a cikin “Raddul Azhan”. Da yin bayani a kan maudu’ai daban daban in Allah Ya yarda.
            Wannan littafi mai suna Gabatarwa kamar duwatsu ne na ginin da za mu yi a littafai na gaba masu zuwa, kamar yadda za mu gani a cikin littafin takaitattun bayanai ne na rahotannin taruka, da tattaunawa a jaridu irin su Gaskiya ta fi Kwabo da jaridar Amana da Makaloli da bayanan rediyo, kuma munyi kokarin kawo shekaru wani lokaci har da wata da ranar da aka buga jaridun da muka kawo wani bayani mai tushe irin wannan saboda masu tsokaci a kan irin wadannan bayanai domin tabbatar da gaskiyar abinda ya faru, wannan shi ya sa za mu fara da bayanin taro kamar haka:

No comments:

Post a Comment