TARON JAMA’ATU NA 14/08/2009
A taron da aka yi ranaku biyu a dakin taro na
Jama’atu Nasril Islam a Kaduna, a ranakun Juma’a da Asabar na 14/08/2009 da
15/04/2009 wanda Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar ya
Jagoranta, domin tattauna wasu muhimman abubuwa.
abubuwan da aka tattauna muhimmai guda biyu ne:
1.
maganar ganin watan azumi,
saboda alokacin mako guda ya rage a dauki Azumin watan ramadan.
2.
sai kuma batun masu yin Tafsirai a watan azumi ana sawa a gidajen Rediyo, a yi masu nasiha da su rinka fadar abin da Allah ya ce su daina sa son zuciya suna sukan juna da
kafirta Musulmi.
Allah ya saka ma shugaban taro da alhairi da
sauran Sarakuna da malamai da manyan ma’aikata da sauran jama’ar da suka
halarci wurin wannan taro da niyya mai kyau.
Sai dai a wurin wannan taro da aka fito da
sakamako mai kyau, ko da shike ba a yi la’akari da batuncin da ake yi a
tafsiran da ake sawa a gidajen rediyo na yau da kullum ba, na wadanda suke raye da wadanda suka mutu.
Har ila yau da rubutaccen tafsirin Hausa, da na
Larabci, na Malam Abubakar Gumi, wanda ya tara wadannan maganganu na batanci,
wanda shi almajiran Malam Abubakar Gumi suke dubawa su fassara, su yi sharhi da
abin da suke cira daga bakinsa a kullun.
Tare da cewa a wannan karon kamar an dauki
tsattsauran mataki na yin gyara, amma sai tsawatarwar ta zamo kamar an kara ma
tabo ruwa ne, don kuwa har sabbin masu batancin aka karo, suna cewa babu wanda
ya isa ya hana su fadar abin da -wai- Allah ya ce.
Allah ya
sani wasu wadanda ake sa tafsiransu a gidajen rediyo wadanda da ma ba a san su
da batunci ba, sai dai kokarin kare kai, suna iyakacin kokarinsu a wurin
tafsiransu, Allah ya kara ba su hakuri, don kuwa mun san sun yi shiru ne don
martaba kiran da Mai alfarma Sarkin Musulmi da sauran sarakuna suka yi, da kuma
kokarin da a ke yi a kullum don samun hadin kai a tsakanin musulmi, ba a
Najeriya ba kawai a duk kasashen Musulmi na duniya don magance fitintunun da
suka shama kowa kai wanda ake jinginawa ga Musulmi. Allah ya sauwake.
Amma ya kamata shuwagabanninmu su sani cewa
magance rikici a tsakanin malamai a kasar nan ba abu ne mai sauki ba, don ya
riga ya sami gindin zama a tsakanin al'umma, kuma wasu suna cin gajiyarsa, don
haka ya zama dole mu dauko dan takaitaccen tarihinsa, da bayanin inda aka bi
aka bibbirne shi a cikin wasu tafsirai kamar "رد الأذهان" na Malam Abubakar Gumi, da
sauran wasu littafai irin shi, don a tono shi a nuna ma Jama’a inda cutar take.
Kafin mu shiga cikin wannan tafsiri yana da kyau
mu dan tabo tarihin wannan harka ta Wahabiyanci yanda ta shigo kasar nan, da
kuma yanda Allah Madaukakin Sarki ya tsare kasarmu, daga irin abin da ya sami
Al’ummar Musulmi a kasar Hijaz kafin a canza mata suna zuwa kasar
Saudiya.
halin zamantakewa A shekarar 1962 zuwa 1965
Dr. Ahmad Gumi ya taba fadi a wurin tafsirinsa na shekara ta 2006 cewa: “Mahaifinsa Malam Abubakar Gumi, shi da Firimiyar Jihar Arewa Mai Girma Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto sun hada hannu don kawo gyara a cikin Addinin Musuluci sai Kafirai suka kashe shi”.
Da ya ke Dr. Ahmad Gumi ya tabo tarihi, kuma ta
yiwu labari aka ba shi, don lokacin yana karami, kuma harkar gwagwarmayar
Musulunci daga baya ya kutsa kai a ciki da rana tsaka, kuma kasancewar
almajiran mahaifinsa yawancinsu yara ne irinsa, kuma ga alama bai bi wadanda a
ka yi abin da su ba don ya san gaskiyar al’amarin saboda fahimtar su ta addini
ba daya ba ce.
Saboda haka sai muka ga tunda ga wata gaba ta
samu ta neman gyara, wanda sai an san ciwo za a san maganinsa, sai muka ga ya
dace mu gaya masa abin da bai sani ba, don kar mu shiga cikin fushin da Allah
ya keyi da masu boye Ilimi, don ta haka za a gane tuni aka gama gudu, a yanzu
zamiye a ke yi.
Ba za mu koma ga tarihin yanda aka kafa daular
Wahabiyanci a kasar Hijaz ba, wanda a yanzu ake kiranta da suna kasar Saudiya,
a zamanin Sarki Abdul-Aziz, wanda aka hallaka dubban musulmi musamman Ahlul-Baiti
a garin Makka da Madina - bayin Allah wadanda aka zarge su da bauta ma kabarurrukan
salihan bayi mun san Dr. Ahmad Gumi yana da wannan tarihi duk da a na boye shi
a Saudiya ba su son a bayyana irin tabargazar da suka yi domin yada sharri ba
shi da kyau a addinance.
Shi Malam Abubakar Gumi wanda yake da ra’ayin
Wahabiyanci, a shekara ta 1962 aka nada shi Alkalin-alkalai na Jihar Arewa,
shekara guda bayan da aka nada shi, ya ba
Firimiyar Jihar arewa Mai Martaba Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto
shawara da a shirya taron malamai na Arewa don tattauna wasu matsaloli kamar
yadda bayaninsa a wurin taron ya nuna.
An yi wannan taro na farko a Ranar 23/08/1963
wanda aka yi kwanaki uku ana yi, malaman da aka gayyato zuwa wurin wannan taro
(47) ne amma malamai biyu ne kawai ba su sami halarta ba. Shugaban taro shine
Wazirin Sokoto Shaykh Malam Junaidu, babban bako mai jawabi shine Firimiyan
Jihar Arewa Alhaji Sir Ahmadu Bello Sardauna.
Abubuwan da aka tattauna a wurin taron sune: Maganar
Hajji, Zakka, Sadaki, da Azumi, ga kadan daga jawabin Mai Martaba Sir Ahmadu
Bello a wurin wannan taro inda yake cewa:
“Bambancin darika, ko na Mazhaba ba zai hana mu
taruwa wuri daya mu duba abin da zai kyautata addininmu ba, kamar yadda bai
hana mu haduwa a masallatan Juma’a da sauran Masallatai ba, haka nan bai hana
mu haduwa a sauran wurare na ma’amalar yau da kullum ba.
Ta haka ne Musulmi suka kange Addininsu daga sukan wasunsu, darikoki
da Mazhabobi sun banbata da Juna, amma manufar su duka guda ce”.
Wannan wani yanki ne daga jawabin Alhaji Sir
Ahmadu Bello Sardauna, Allah ya saka masa da alhairi, wannan jawabi yana nuna
halin zamantakewar al’ummar Musulmi a shekara ta (1963) yadda ‘Yan darika da wadanda
ba ‘yan darika ba suke zaune lafiya, suke yin sallah a Masallaci daya. A gaban
Malam Abubakar Gumi aka yi wannan jawabi.
Amma sai ga shi a cikin shekaru biyu kacal
al’amura sun canja, a taron malamai na biyu da aka yi a shekara ta 1965 wanda
aka kira malamai (101) duk da shugaban taro wazirin
Sokoto Shiekh Junaidu, Allah Ya gafarta masa, amin.
Ajandar taro magana ce a kan kabalu da Sadalu da
kuma maganar darikoki, da maganar mayaudaran malamai, da masu tafsirin kur’ani
da barna da maganar jahilan masu wa’azi, da maganar barin aiki da littafan malaman
Sunna, da maganar tarbiyya batacciya da ta asali, da bincika malamai masu
haddasa fitina.
Daga jin yanda ajandar taron ta koro; tana nuna alfijir din Wahabiyanci ya fara
kunno kai a kasar nan, don haka sai kiyayewan Allah don idan aka gwama ajandar da
jawabin da Mai Martaba firimiyan Jihar Arewa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto
ya yi, za a gane tafiya ta fara sauyawa.
Zamu kawo kadan daga cikin abinda yace a wata
doguwar huduba da yayi a Ranar Talata 15 ga watan Yuni 1965 wanda yayi dai dai
da 14 ga watan Safar Hijira 1385, Jawabin wanda aka rubuta da hausa yana da sadara
(152) ga kadan daga cikin wannan Jawabin wanda yafi tsorata Mahalarta wannan
taro:
“Malik bin Anas ya ce: Ya halasta a kashe Sulusi watau Kashi daya daga uku na Jama’a masu fitina, domin kashi biyu su rayu cikin kwanciyar hankali”.
Idan muka ji dokokin da aka fito da su a karshen
taron, za a iya gane wadanda a ke zargi da kawo fitina a wannan lokacin, an dai
kafa dokokin ne kamar haka:
-
an hana ko wane limamin da zai jagoranci Sallah, tare da jama’a yayi kablu,
idan ya ki bari za a cire shi.
-
an hana Malamai kai ziyarce-ziyarce wajen muridan su, in suna son wani
abu, sai muridai su tafi su iske su.
-
An hana tarbiyya
wanda ake yin tawassuli wanda ya yi da wanda ya sa aka yi sun kafirta.
-
An hana yin tafsiri da wa’azi sai wanda aka
jarraba shi ya ci jarabawa….
Abubuwa goma shadaya ne aka cimma matsaya a kansu
na karshensu shine: Hana ginin Masallatai barkatai”.
Bayan wadannan Dokoki da aka kafa sun fara aiki
da wata shida, sai kasa ta fada cikin wata fitinar, wato juyin mulki na sojoji,
wanda ta kai ga sanadiyyar rasuwar Firimiyar Jihar Arewa Sir Ahmadu Bello
Sardauna a shekara ta 1966, Allah ya gafarta masa Amin. wannan juyin mulki ya jawo
yakin (Biyafara) na kusan tsawon shekaru uku.
Wannan hali da kasa ta shiga sai ya kawar da
hankali ga batun Sallar kablu da maganar Tarbiyya da maganar shayhunai masu
kawo ziyara, sai aka mayar da hankali wajen neman hadin kan al’ummar Jihar
Arewa, da na Jihar Yamma, ba tare da yin la’akari da wannan musulmi ne ko
wannan ba musulmi ba.
Bayan an karkasa Gwamnatin Jihar Arewa zuwa
Jihohi guda 5 an soke tsarin En’e-En’e wanda ya takaita ikon sarakuna a
sha’anin mulki, sai ya zama ko wace jiha tana cin gashin kanta, tare da
sarakunanta, wadanda aka canja masu suna zuwa Sarakunan Gargajiya, a maimakon
Sarakunan Musulunci, amma Malam Abubakar Gumi, an barshi a matsyin Alkalin-Alkalan
Jihohin Arewa.
Jama’atu Nasril Islam mai helkwata a garin
Kaduna, wanda Firimiya Sir Ahmadu Bello Sardauna ya kafa a shekara ta 1961
Allah cikin ikonsa ya sa ba a ci gajiyarta ba, sai bayan rasuwarsa, inda ta
zama ita ce cibiya guda daya tal da ta saura don hada kan al'ummar Musulmi na
jihohin Arewa, a karkashin sarkin
Musulmi Alhaji Sir Abubakar na uku, tare da sarakunan jihohin Arewa, da manyan
malamai, da wasu daga cikin ma’aikatan Gwamnati masu sha’awar bayar da
gudummuwa a harkokin musulunci.
Wannan kungiya wanda a cikin kudurorinta duk mai
cewa: “Lailaha Illallahu, Muhammadur Rasulul Lahi” dan ta ne, ko wace irin
mazhaba yake bi, ko wace irin darika yake yi, samun wannan kungiya ta Jama’atu
ya samar da kyakkyawar fahimta tsakanin malamai da sarakuna, amma bai kawar da
irin tsanar da ake yi wa almajiran Shayhu Ibrahim Kaulaha ba, sai da Gwamnatin
tarayya a karkashin Janaral Yakubu Gawan a shekara ta 1968 ta tura wata tawaga
ta musamman a karkashin jagorancin Malam Aminu Kano zuwa Kaulaha a kasar
Senigal wurin Shayhu Ibrahim (R.A) don neman a yi wa Najeriya du’ai ta sami
galaba a kan ‘yan tawaye a kawo karshen yakin Biyafara.
wannan ziyara ya haifar da sake kulla sabuwar alaka
da Gwamnatin Gawan ta yi da Shayhu Ibrahim Kaulaha (R.A) kuma ya kawar da karan
tsanar da ake sa wa almajiransa masu yin Sallar kablu a wancan lokacin, da ci
gaba da kawo ziyarar shaihunnai da sharifai zuwa kasar nan wanda aka hana a
shekara ta1965.
A sakamakon haka ne Shaykh Malam Ummaru Sanda
limamin Sojoji a garin Kaduna daya daga cikin jamian gudanarwa na Jama’atu
Nasril Islam ya rubuta wata makala a shekara ta (1968) mai dauke da taken: MATSAYIN
kABLU DA SADALU A CIKIN AL-kUR’ANI DA SUNNAR MANZON ALLAH mai shafi (18)
wanda aka rika bugawa a cikin Jaridar gaskiya
ta fi Kwabo ta wannan shekarar, wannan jawabi na Malam Ummaru Sanda ta jawo
mayar da martani daga malamai a jaridu da littafai, musamman saboda in da ya
nuna yin sallar kablu ita ce sunnar da tafi shahara.
Tare da cewa wannan jawabi na Malam Ummaru Sanda
ta kawar da kyamar da ake yin ma masu yin sallar kablu, sai dai kuma ta sanya
an bude wani sabon shafin na shiga cikin darikar Tijjaniya ita kanta, domin a
jawabin rufe muhawara, wanda Kanfanin buga jaridar Gaskiya ta fi Kwabo ta dauki
alhakin kawo muhawarorin ta nuna cewa za ta rufe wannan muhawara da ra’ayin
Malam Abubakar Gumi ne a matsayinsa na Alkalin-Alkalan Jihohin Arewa.
A jawabinsa wanda aka buga a shafi na (9) na jaridar Gaskiya ta fi Kwabo
ta ranar Litinin (4) ga watan Oktoba, 1971, mai dauke da taken: kabalu da
sadalu ko wannen su yana da asalinsa.
Bayan ya fadi hujjojinsa a game da kabalu da
sadalu, sai a karken jawabin ya jawo hankalin wasu jama’a da cewa:
Mai sharia Malam Bashir Sambo - Allah ya gafarta
masa amin - ya fada a wata hira da Jaridar Gaskiya ta fi Kwabo ta yi da shi a
ranar 22/08/2005 a shafi na 12 da 13 a fira ta 4 game da farkon rikicin darika
da Malam Abubakar Gumi, ya nuna cewa
yana tare da Malam Gumi a Jama’atu Nasril Islam tun a shekara ta (1968) ga abin
da ya ce ya fara jawo rikicin:
“To ka san yadda abubuwa suka faro tun asali, mutane ba su gane ba,
lokacin da shi Sheikh Gumi ya ke Grand Kadi ya samu dama ta yin wa’azi da
sauransu, ya nemi ya yi amfani da fahimtarsa, rigimar da aka fara yi ita ce,
lokacin da yake wa’azi a masallacin Sarkin Musulmi Bello, inda ya yi maganar
Jauharatul Kamali yace Surguduballe ce, musamman kan wata kalma “ASkAM” wannan
shi ne farko farin rikicin da ya fito”
Wannan shi ne jawabin Malam Bashir Sambo, idan an
duba jaridar ta shekarar 1968 za a ga inda Malam Abubakar Gumi ya ke cewa da za
a canja wannan kalmar a ce"صراطك تم المستقيم" da babu aibi a karanta
wannan salati a cikin wazifa.
Sai dai malamai sun maida masa da martani game da
wannan kalma ta"الأسقم" daga cikin wadanda suka mayar da martani akwai
Shaykh Malam Atiku Kano wanda ya rubuta littafi mai suna:
"تنبيه النبهاء ليلاً يغتروا بأقوال السفهاء".
Wanda ya kulle kofar muhawara game da wannan
kalma ta "الأسقم" shine shayhin Malamin Larabci a Jami’ar Bayaro
ta Kano prof. Aliyu Na’ibi
Suwaid, a inda ya rubuta Littafi mai suna:
"تعليق لغوي على كلمة الأسقم الواردة في الصلاة المعروفة بجوهرة الكمال"
Jawabin da ya yi a wannan dan karamin littafi
wanda a ka buga a shekara ta 1977 wanda ya yi daidai da (1409) Hijiriyya ya
rufe bakin Malam Abubakar Gumi, bai sake magana a kan wannan kalmar ba, tare da
cewa bai kawo karshen rigimar ba, don manufar shi a koma ne gaba daya, a
rungumi akidar Wahabiyanci a wannan kasa wanda aka so a baya a yi amfani da Mai
Martaba Firimayar Jihar Arewa don yada ta.
A
shekara ta (1970) Malam Abubakar Gumi ya wallafa wani littafi mai suna: "العقيدة الصحيحة" daga sunan da aka sanya ma
wannan littafi za a fahimci cewa; a na shirin kawo ma al'ummar Musulmin kasar
nan wata sabuwar fahimta ce game da Ilimin Tauhidi sabanin ta Imamul Ash’ari
wanda su ka rayu a kanta wanda ita ce mafi yawan kasashen Musulmi su ke kai, in
banda kasar Saudiya dmai bin sabuwar akida ta dan Abdul-Wahabd.
Sai dai wannan littafi wanda a ka so ya zama abin
yin aiki da shi a Makarantun Zaure da na Nizamiya Allah bai sa ya sami karbuwa
ba, domin hatta a wurin almajiran malamin littafin na shan suka saboda dalilai
masu dama.
Har ila yau malamai da yawa sun kalubalanci
wannan littafi saboda dinbin kurakuran da ya taras a ciki, a maimakon akidar da
littafin ya kunsa ya zama sahihi, sai ya zama fasidi, kamar yadda Shaykh Malam
Sani Kafanga ya rubuta wani littafi don yin raddi ga wannan littafin ya fada : "المنح الحميدة في الرد على فاسدة العقيدة" mai son karin bayani sai ya
nemi wadannan littafai guda biyu da na Malam Abubakar Gumi da na Shaykh Malam
Sani Kafinga, Allah ya gafarta masa, amin.
Malam
Abubakar Gumi a kokarinsa na tabbatarda Wahabiyanci da shafe darikar Tijjaniya
a doron kasa, a shekara (1973) a wurin Karatunsa an yi masa tambaya game da
karanta Salatil Fatihi sai ya karanta sannan yace: "Wannan salatin
Annabina lafuzzanta masu kyawuna, sai dai cewa da a ke yi an yi ma Ahmadul
Bakariy wahayinta shi dai ak kahirci, da kuma cewa karanta ta yahi karanta Al-kur’ani,
ku duba cikin littafin Jawahirul Ma’ani”.
Da
farko kamar yanda muka fadi a baya Malamin ya fara ne da kalmar (Al-askam) ta
cikin (Jauharatul Kamali) inda ya yi gyara ya ce da za a ce"صراطك المستقيم" da yafi, a lokacin (Salatil
Fatihi) bai ce ga aibin ta ba sai anan, shima anan ba cewa a ka yi karanta ta
yana da aibi ba, imma da shi ba a riga an gano ba a lokacin.
To, amma duk da haka wannan jawabin
na sa, ya jawo ka-ce na-ce da shi Malamin, har da wadanda ba ‘yan darikar ba
abokan aikinsa a Jama’atu Nasril Islam, kamar mai shari’a Malam Bashir Sambo,
wanda ya fadi a wata hira da Jaridar Gaskiya ta fi Kwabo ta yi da shi ta ranar
24/08/2005 a shafi na (13) a inda yace:
“Na taba daukar Jawahirul Ma’ani na tafi wajen Malam Gumi lokacin
da ake rigimar Salatul Fatihi” ko saukakkiya ce ko kuma wanda ya karanta ta
yana da lada kaza.
Na nuna masa wani
shafi da aka yi bayanin falalarta, wanda
a karshen falalar sai aka ce, mai yiwuwa ne wani wanda ganewa ba ta ishe
shi ba ya ce: wannan salatin ita zai
ta’allake mata, tun da ta fi kur’ani, ya ce ko da aka yi maganar falala, babu
yadda za ayi salatil fatihi ta fi kur’ani, ba wani abin da
ya fi kur’ani, a cikin littafin a ka fadi haka..”
Ya ci gaba yana tambayar Malam Abubakar Gumi da
cewa: me ya sa ba a karanta komai har karshe don mutane su amfana?”
Wannan ita ce magana ta adalci, daga bakin malami
adali mai shari’a Malam Bashir Sambo Allah ya yi masa gafara, hirar da a ka yi
da shi ta na da tsawo, sai dai kawai a nemi jaridan har ya kawo masa misali da
yanda ya ke yawan son a karanta (Salatun Tunajjina) alhali duk
jirgi daya ya kwaso su da Salatil Fatihi, har ma Salatil Fatihi ta dara don an
san wanda aka ruwaito daga gareshi.
CIRE MALAM GUMI A ALKALIN ALKALAI A shekara ta 1975
Sauke Malam Abubakar Gumi a Matsayin Alkalin Alkalai
na Jahohin Arewa a shekarata (1975)ya sa ya rasa wata dama da ya ke da ita ta
fadar abin da ya ke so, ba tare da jin komi ba, saboda kariya da yake da ita ta
huskan jami’an tsaro. da kuma alkalai da su ke karkashinsa, saboda haka sai ya
yi kokarin samar da wata kungiya ta ‘yan bangarsa a shekare ta (1976), shi da
kansa Malam Abubakar ya taba gaya ma
wani babban mai sarauta, da ya tambaye shi dalilin kafa kungiyar Izala, sai ya
gaya masa cewa ya sa an kafata ne don ta rika bashi kariya saboda ya ga ‘yan darika
suna barazanar hallaka shi.
Babu shakka wannan kungiya ta Izala ta bayar da
kariya ga Malam Abubakar Gumi ta wajen yada Akidar Wahabiyanci a wannan kasa,
don ta fito da karfinta, ba ta shakkar fadar duk abin da ta ga dama. Misali a wurin wani taro da Jama’atu Nasril
Islam ta kira a shekara ta (1977) Alhaji Bala Sirajo daya daga cikin jagororin kungiyar
Izala na hannun dammar Malam Abubakar Gumi ya tashi a taron jama’a ya wanke wa
sarakunar da suka halarci taron hannu a ka, babu bakar maganar da bai fada masu
ba, wanda ya tayar da hankulansu, amma a karshe sai a ka tsayar da shawarar
cewa a jawo su ne, don a tafi tare da su a cikin harkokin Jama’atu, wanda ya kara
masu karfin guiwa, sarakuna suka shiga jin tsoransu.
DUBA
YANDA ZA A SAMI MATSAYA A 1977/ 78